News
An Gurfanar da Mutane 2 A Kotu Bisa Zargin Satar Koko
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a ranar Juma’a ta gurfanar da wasu mutane biyu a gaban wata kotun majistare da ke Ile-Ife bisa zarginsu da fasa wani gida tare da sace waken koko na Naira 250,000.
Wadanda ake tuhumar, Felix Philip, mai shekaru 20 da Michael Julius, mai shekaru 20, suna fuskantar tuhuma guda uku da suka hada da hada baki da kuma sata.
Sai dai sun musanta zargin da ‘yan sanda suke yi musu.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Abdullahi Emmanuel, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Satumba, 2023, a kauyen Mosaajo, Ile-Ife.
Emmanuel ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun shiga gidan wani Olajide Rotimi inda suka sace buhu daya da rabi na koko wanda kudin sa ya kai naira N250,000.
Laifukan, in ji shi, ya sabawa sashe na 390(9), 411, da 516 na dokokin manyan laifuka na Osun shekarar 2002 kuma ana hukunta su.
Alkalin kotun, Kikelomo Adebayo, ta bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi N50,000, tare da mutum daya da zai tsaya masu.
Adebayo ta ce dole ne wanda zai tsaya masu ya rantse da wata takardar shaida kuma ya zauna a cikin hurumin kotun, baya ga shaidar takardar shaidar biyan haraji na shekaru uku.
Daga nan ta dage sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Oktoba.
Wani labarin kuma Cutar Mashako Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 14 A Jihar Jigawa
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro