News
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun:Allah ya yiwa shugaban ƙungiyar dattawan Jihar Jigawa rasuwa.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Allah ya yiwa shugaban ƙungiyar dattawan Jihar Jigawa. Alhaji Suleimanu Baffa rasuwa. Za’aji Jana’izarsa da misalin ƙarfe 4 na Yamma a Ƙofar Kudu dake fadar mai martaba Sarkin Kano.
An haife shi a shekarar 1938 a garin Auyo, Ya rasu yana da shekaru 85, ya taɓa riƙe shugaban Ma’aikatar Buga kuɗi da Adana muhimman takardu ta Ƙasar nan (Minting and Printing) ya zama Permanent Sakatare yana da shekaru 30, ya taba zama Darakta a bankin UBA, an naɗa shi a matsayin uban Bankin Jigawa Savings And Loan, lokacin mulkin tsohon gwamna Sule Lamido.
Allah ya jiƙansa ya gafarta masa. Amin
Advertisements
