News
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Bada Umurnin Gaggauta Gyara Asibitin Sir Sanusi General Hospital
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a gaggauta gyara babbar asibitin kula da lafiyar al’ummar Kano wato”Sir. Sanusi General Hospital” a kokarin sa na kara bunkasa harkokin kiwon lafiya.
Wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa da jaridar Inda Ranka, yace Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar ba-zata da ya kai asibitin.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin N-Power har illa-masha-Allah.
Gwamnan wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda asibitin ya lalace, Inda nan take ya yi alkawarin cewa za a fara aikin gyaren ne domin tabbatar da majinyata da ma’aikatan lafiya sun samu yanayin da ya dace a asibitin.
“Dole ne in gaya wannan asibitin, saboda abin da na gani da idona ya ban tsoro sosai da sosai, ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatinmu za ta kawo muku agaji nan bada jimawa ba, bayan wannan ziyarar.”
“Zan umurci ma’aikatar lafiya da dukkan hukumomin da ke karkashinta da su shirya yadda za a gudanar da aikin gyaran dakunan kwanan marasa lafiya, bandakuna da dakunan yin tiyata” in ji Gwamna Abba Kabir.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a gaggauta daukar wata ma’aikaciyar lafiya ta wucin gadi mai suna Khadija Adam, Saboda yadda take tallafawa marasa lafiya.
Ya kuma yi wa marasa lafiya dake asibitin fatan samun sauƙi, sannan bada kyautar naira dubu ashirin ga kowanne mara lafiya dake asibitin a matsayin tall
afin gaggawa .
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
