Connect with us

Business

kamfanin BUA ya kara farashin Taliya,Sukari da kuma Fulawa bayan rage kuɗin siminti

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Kwanaki kadan bayan sanar da rage farashin kuɗin siminti, kamfanin BUA cikin sirri ya kara farashin kayan abinci, musamman buhun sukari da buhun fulawa da kuma katon din taliya , kamar yadda bincike ya nuna.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa a ranar 1 ga watan Oktoba ne mahukuntan kamfanin simintin BUA suka sanar da rage farashin siminti zuwa Naira 3,500 kan kowace buhu.

Advertisement

Ma’aikatan Hukumar Kwashe Shara ta Kano Sun Gudanar Da Zanga-zanga Kan Rashin Biyan Su Hakkokin Su 

Haka kuma Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Sanarwar ta yi matukar farantawa jama’a sai dai kuma dillalan kamfanin suna ta fadawa abokan cinikinsu cewa ragi farashin ya shafi wadanda suke zuwa kamfanin su sayo kayansu ne kai tsaye.

Sai dai wani bincike da wakilin jaridar Inda Ranka Muhammad Muhammad Zahraddin ya gudanar ya nuna cewa kamfanin BUA ya yi karin kuɗi ga sukari da fulawa da kuma taliya .

Advertisement

 

Wakilinmu wanda ya zagaya da wasu shaguna a shahararriyar Kasuwar singer da ke Jihar Kano, babbar kasuwar kayan abinchi a Arewacin Najeriya, ya lura cewa farashin buhun sukari, fulawa da katon taliya spaghetti ya karu da N3,500, N2,000, da kuma akalla N1000 .

Advertisement

 

Gwamnati da Majalisar Dokokin Kano zamu kafa tarihin da ba a taba irinsa ba- Mataimakin gwamna

Advertisement

 

Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa, a kwanan baya an sayar da sikari kan Naira 44,000 kan kowanne buhu, sai taliya Naira 8,100 kwali, sai buhun fulawa kan Naira 32,500, yanzu haka ana sayar da sikarin Naira 47,500, taliya N9,000, sai kuma buhun fulawa N34,500.

Advertisement

 

Wani dilan kayayyakin abinci na BUA a Kano ya shaida wa wakilinmu cewa, an karawa kayayyakin kamfanin BUA kuɗi ne bayan da kamfanin ya sanar da rage kuɗin siminti.

Advertisement

 

 

Advertisement

A cewar dilan, wanda ya nemi a sakaye sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, yace an karin kuɗi kayan ne a makon da ya gabata.

 

Advertisement

 

Ya tabbatar da cewa farashin katon din taliya IRS, wadda kamfanin BUA ke samarwa, yanzu ta koma Naira 9,000 a farashin kamfani, yayin da a kwanan nan aka sayar da shi akan N8,400 kwali, wanda ke nuni da cewa zata iya kai wa. zuwa N10,000 a farashin sari.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ya kuma ce “An sami karin kuɗin ne wannan makon. Farashin buhun fulawa yanzu ya haura zuwa N34,500 sabanin N31,000 zuwa N32,000 da aka sayar a makon jiya. Kimanin Naira 2,000 aka kara akan buhun fulawar kuma haka ma farashin kamfani ne.

Advertisement

 

” Game da sikari, babu tsayayyen farashi amma ana sayar da shi har Naira 48,000 yanzu a kasuwa, maimakon Naira 44,500 zuwa N45,000 a kan kowacce buhu a makon jiya. Wani ya ce mani yana sayar da shi akan Naira 46,500 kan kowace buhu.

Advertisement

 

“Ina kuma so in gaya muku cewa duk waɗannan farashin farashin kamfani ne,” in ji shi.

Advertisement

 

Hakazalika binciken da muka gudanar ya nuna cewa tuni farashin kayayyakin ya yi tashin gwauron zabi a wajen masu bada sari a cikin birnin Kano.

Advertisement

 

Duk Kokarin samun kamfanin BUA ya ci tura.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending