Connect with us

News

Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a jahar Neja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

An yanke wa wasu ‘yan Nijeriya su biyar ɗaurin shekara 12 a gidan yari bayan kama su da laifin tono ƙoƙon kan wani mutum domin yin asirin yin arziƙi.

Mutanen sun tono ƙoƙon kan ne domin kai wa wani boka, wanda ya ce ana buƙata domin yi musu asirin zama masu kuɗi.

Advertisement

 

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 67 a duniya

Mutanen waɗanda aka kama su da ƙoƙon kan a cikin wani buhu, sun amsa laifinsu a kotu.

Advertisement

Mai gabatar da qara ya shaida wa kotu a jihar Neja da ke arewacin Nijeriya cewa mutanen sun zaƙulo gawar ce a wata maƙabarta bayan binne ta na tsawon shekara uku.

 

Advertisement

“Waɗanda ake zargin sun ce bokan ya musu alƙawarin cewa za a raba dukiyar da aka samu daga tsafin a tsakaninsu, inda ya buƙace su da su kawo ƙoƙon kan mutum,” in ji Jaridar Daily Punch.

 

Advertisement

A cikin watan Satumba ne jami’an tsaro suka kama matasan biyu lokacin da suke ƙoƙarin bai wa wani mutum ƙoƙon kan domin isarwa ga boka.

 

Advertisement

Wata kotu a garin Minna ta jihar Neja ce ta ce ta kama mutanen da laifin haɗa kai wajen aikata laifi, da yin kutse a maƙabarta da kuma mallakar ƙoƙon kan bil’adama ba bisa ƙa’ida ba.

 

Advertisement

 

Sai dai ba a samu nasarar kama bokan ba.

Advertisement

 

Tsafe-tsafe dai wani lamari ne da aka sani sosai a Nijeriya, inda hatta wasu mabiya addinan Musulunci da Kirista sukan yi imani da shi, kamar yadda bincike ya nuna.

Advertisement

 

Yawancin sun yi imani da cewa yin tsafi da jikin ɗan’adam na kawo kuɗi, lamarin da ke ƙara iza wutar kashe-kashen mutane kamar mata da yara da masu nakasa domin tsafi.

Advertisement

 

Haka nan akan samu mutanen da ke shiga sana’ar sayar da sassan jikin ɗan’adam domin samun kuɗi.

Advertisement

 

Ana kuma ganin cewa talauci da kwaɗayin kuɗi na daga cikin abubuwan da ke iza wutar tsafe-tsafen a Nijeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending