News
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 67 a duniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na taya jagoran tafiyar Kwankwasiyya, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran jam’iyyar na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Alhaji Abba Kabir ya bayyana Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin mutum mai aki’ida, jajircewa, hakuri, juriya da hangen nesa.
An Cafke Wasu Mutane Biyu Bisa Zargin Kashe Wata Matar Aure ‘Yar Shekara 24 A Jahar Borno
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Jaridar Inda Ranka.
“Akidar ka ta gina dan Adam da kishin talakawa babban abin koyi ne ga dukkan shugabannin wannan zamani” in ji Gwamna Abba.
Yadda Wani Kwale-kwale ya Kama da Wuta Yana tsaka da Tafiya a Ruwa a Jihar Neja
Gwamna Abba Kabir ya kara da cewa manyan nasarorin da Kwankwaso ya samu na nuni da irin yadda yake nuna rashin son kai da kishin kasa wajen yiwa jiharmu da kasa baki daya hidima a koda yaushe.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya kara wa Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso lafiya da basira domin ya jagoranci magoya bayansa zuwa babban mataki cikin kankanin lokaci da yardar Allah.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
