News
An Cafke Wasu Mutane Biyu Bisa Zargin Kashe Wata Matar Aure ‘Yar Shekara 24 A Jahar Borno
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno a jiya ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu, Adamu Ibrahim da Bukar Wadiya bisa zargin kashe wata matar aure Fatima Alhaji-Bukar ‘yar shekara 24 a duniya.
Marigayar dake zaune a Dikechiri a unguwar Bayan Gidan Dambe a cikin birnin Maiduguri a jihar Borno.
Bai Kamata A Ce Shugaban Kasa Ne Yake Nada Shugaban INEC Ba – Farfesa Attahiru Jega
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Sani Kamilu, ya rabawa manema labarai a Maiduguri.
A cewarsa, wacce abin ya faru akan ta, tana auren Adamu Ibrahim, wanda shi ne babban wanda ake zargi da aikata laifin.
A cewar majiyar yan sanda, binciken farko da aka yi ya nuna cewa kafin faruwar lamarin, ma’auratan sun samu sabani a cikin gida kan zargin karin aure da mijin ke shirin yi.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro sunyi wa gidan da lamarin ya faru kawanya, a yayin bincike an gano wasu kayayyaki da suka hada da tabarya, jaka, igiya, da kafet cike da jini, wuka, da motar Honda a gidan da lamarin ya faru. Kakakin yan sandan ya ce babu wata shaida da ta nuna cewa an karya kofar gida kafin shiga, kuma mijin ne kawai ke da mabudin gidan.
A Wani labarin kuma Bai Kamata A Ce Shugaban Kasa Ne Yake Nada Shugaban INEC Ba – Farfesa Attahiru Jega
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
