News
Yan Bindiga Sun Sace Babbar Malama A Jami’ar Jihar Nasarawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A halin yanzu an samu rudani a jami’ar jihar Nasarawa dake garin Keffi (NSUK) bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da daya daga cikin manyan malamai Dokta Comfort Adokwe.
A ranar Lahadi da daddare ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da Adokwe, malami a tsangayar gudanarwa na jami’ar, kuma mataimakiyar darakta a fannin nazarin jinsi, a gidanta da ke Angwan Jaba a garin Keffi.
Yan Ta’adda Sun Kashe Shugaban Karamar Hukumar Da Mutane 8 A Katsina
Shugaban kungiyar ci gaban al’umma, Kwamared Ali Sule, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Post
ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan malamar ne da daddare suka garzaya da ita inda ba a san inda suke ba.
Ya ce masu garkuwan sun yi harbin iska da dama kafin daga bisani su tafi da malama.
Ya ce, “Gaskiya ne, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da ‘yar uwarmu mai kauna, Dokta Comfort Adokwe a daren jiya a gidanta da ke Angwan Jaba a nan Keffi. Muna addu’ar Allah ya jikanta, ya tsare ta, ya kuma dawo mana da ita lafiya. Muna kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye su dawo da ita lafiya.”
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa lamarin ya zo ne mako guda da sace daliban jami’ar kimanin hudu a dakin kwanan .
Wadanda suka sace daliban hudu sun bukaci a biya su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa domin sako daliban.
An ruwaito cewa wani shugaban kungiyar dalibai a makarantar ya tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi hukumomin makarantar inda suka bukaci a biya su kudin fansa.
A wani labarin kuma Yan Ta’adda Sun Kashe Shugaban Karamar Hukumar Da Mutane 8 A Katsina
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
