Connect with us

News

Yan Ta’adda Sun Kashe Shugaban Karamar Hukumar Da Mutane 8 A Katsina

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kashe mutane tara tare da yin garkuwa da wasu da dama a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.
Leadership ta ruwaito cewa Wata majiya mai tushe ta ce daga cikin wadanda aka kashe har da tsohon shugaban karamar hukumar, Dauda Mai Iyali, lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari garin ranar Lahadi.

Ma’aikatan Majalisun Jihohi Za Su Shiga Yakin Aiki

Majiyar ta ce ‘yan ta’addan sun mamaye yankin ne da misalin karfe 8:00 na dare, inda suka yi ta harbe-harbe a kai a kai, inda suka kashe mutane kusan tara tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadik, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kashe mutane biyar tare da sace wasu biyar a harin.
Ya ce ‘yan sanda na kokarin ceto wadanda aka sace.

Haka kuma Rundunar ‘yan sandan ta na yin namijin kokari wajen ganin an ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba tare da damke wadanda suka aikata laifin.

Advertisement

A wani labarin kuma Ma’aikatan Majalisun Jihohi Za Su Shiga Yakin Aiki

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending