News
Wasu dalibai bakwai a Polytechnic ta jihar Kwara sun samu rauni a yayin da wata gobara ta tashi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu dalibai bakwai a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kwara dake Ilorin sun samu raunuka daban-daban a yayin da wata gobara ta tashi a wani kantin sayar da iskar gas da ke kusa da dakin kwanan dalibai.
Daily Trust ta ruwaito cewa gobarar ta afku ne a Destiny Villa, titin Dola Abimbola, unguwar Elekoyangan a karamar hukumar Ilorin ta Gabas da yammacin ranar Asabar.
Ma’aikatan Jigawa sun nuna damuwarsu kan wa’adin da aka bayar na kammala aikin tantancewa
An kuma bayar da rahoton cewa wata ma’aikaciyar iskar gas ta samu rauni yayin da lamarin ya faru.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Hakeem Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin nan.
Adekunle ya bayyana cewa ” gobarar ta tashi ne a lokacin da wata ma’aikaciyar iskar gas a wani shagon gas da ke kusa da ta ke cike wata silinda.
“Silindar ta fado ta fashe, a lokaci guda tana fitar da iskar gas daga cakin bututun da ake amfani da shi don cikawa. Hakan ya kara ta’azzara gobarar, inda ta yi sanadin jikkatar wasu dalibai bakwai na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kwara da ma’aikaciyar iskar gas.
Ya kara da cewa, “Jimillar asarar kadarorin da aka yi kiyasin an kiyasta kudinta ya kai Naira miliyan 14.6, yayin da jimillar dukiyar da aka ceto ta kai Naira miliyan 72.2.”
Dangane da lamarin, Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John, ya aike da tawagarsa domin duba daliban da lamarin ya shafa ranar Lahadi.
Daraktan ya kuma bukaci jama’a da su ba da fifikon matakan tsaro don hana afkuwar gobara.
A wani labarin kuma Ma’aikatan Jigawa sun nuna damuwarsu kan wa’adin da aka bayar na kammala aikin tantancewa
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Najeriya ta soke nasarar da Gwamnan Filato Caleb Muftwang ya yi a zaɓen watan Maris na 2023.
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ambato tawagar alƙalai mai mutum uku ta bayyana a ranar Lahadi cewa ba a bi ƙa’ida ba wajen tsayar Mista Muftwang a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP kamar yadda sashe na 285(2) na tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Alƙalan sun ce ƙarar da ɗan takarar APC Nentawe Goshwe ya ɗaukaka ta yi nasara saboda batun tsayar da ɗan takara lamari ne da ya shafi lamurran kafin da kuma bayan zaɓe, saɓanin hukuncin da kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta bayar – inda ta bai wa Mista Muftwang nasara.
Tawagar alƙalan ta amince da mai ƙorafin (Goshwe) cewa gazawar PDP na gudanar da bin umarnin wata kotun Filato da ya ce a gudanar da sahihan tarukan jam’iyya a mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma jiha kafin tsayar da ‘yan takara ya saɓa wa doka.
Wannan dalilin ne ya sa kotun ta yi watsi da hukuncin kotun farko a matsayin “wanda bai dace ba kuma ya saɓa da yi wa kowane ɓangare adalci ta hanyar sauraron hujja daga shaidun da aka kora daga shari’ar”.
Kotun ta umarci hukumar zaɓe Inec ta ƙwace shaidar cin zaɓe daga hannun gwamnan mai-ci kuma ta bai wa Nentawe Goshwe na APC.
