News
Zanga-zanga Ta Barke A Filato Kan Kwace Kujerar Gwamna Mutfwang
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata gagarumar zanga-zanga ta barke a Jos, babban birnin jihar Filato, biyo bayan nasarar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr Nentawe Yilwatda Goshwe ya samu a kan gwamnan jam’iyyar PDP, Caleb Mutfwang a hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin soke zaben Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang kan rashin tsari da kuma rashin bin umarnin Kotu.
Wasu dalibai bakwai a Polytechnic ta jihar Kwara sun samu rauni a yayin da wata gobara ta tashi
Kafin yanke hukuncin a ranar Lahadi, an tsaurara matakan tsaro a dukkan muhimman wurare a babban birnin jihar domin dakile duk wata barazanar tsaro.
Amma duk da haka, bayan samun labarin hukuncin kotun, cece-ku-ce ta mamaye jihar yayin da aka ga jama’a tawaga-tawaga suna tattaunawa kan hukuncin.
A karamar hukumar Jos ta Kudu, matasan da ke goyon bayan PDP sun yi dafifi a zagayen Gyel da dama domin nuna rashin jin dadinsu kan hukuncin.
An kuma yi irin wannan zanga-zangar a mahadar Angwan Rukubu da ke Jos ta Arewa da karamar hukumar Riyom ta babban birnin jihar.
A wani labarin kuma Wasu dalibai bakwai a Polytechnic ta jihar Kwara sun samu rauni a yayin da wata gobara ta tashi
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
