News
Tsige Gwamnan Filato: Shari’a ta Zama Akwatin Gawar Dimokradiyya a Najeriya – Shehu Sani
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana bangaren shari’a a matsayin akwatin gawar dimokradiyya a Najeriya
Martanin na zuwa ne a dai dai lokacin da Kotun Daukaka Kara ta Tsige Gwamnan Filato Caleb Mutfwang
Zanga-zanga Ta Barke A Filato Kan Kwace Kujerar Gwamna Mutfwang
Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba inji tsohon Sanatan
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin kotun zaben gwamnan da ta tabbatar da zaben Mutfwang a matsayin gwamnan jihar.
Kotun ta ayyana Dr Nentawe Yilwatda na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar yayin da ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta ba shi sabuwar takardar shaidar cin zabe.
Da yake mayar da martani, Sani ya ce hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.
Da yake wallafawa a shafin na X, Sani ya rubuta cewa: “Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan nasarar zaben gwamnan jihar Filato abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba sannan abin Allah wadai ne.
“Hasken rana mai faɗi na nufin mutane. Bangaren shari’a ya zama akwatin gawar dimokuradiyya.”
A wani labarin kuma Zanga-zanga Ta Barke A Filato Kan Kwace Kujerar Gwamna Mutfwang
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
