Connect with us

News

Hatsarin mota ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum hudu a Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hatsarin mota ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum hudu, wasu da dama suka samu raunuka a kusa da kauyen Dinyar Madiga da ke Karamar Hukumar Takai a Jihar Kano.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ce lamarin ya faru ya yi da wani mai babur dauke da mutum uku ke yunkurin wuce wata motar safa.

Tsige Gwamnan Filato: Shari’a ta Zama Akwatin Gawar Dimokradiyya a Najeriya  – Shehu Sani

Ya ce, “Da isa wurin da lamarin ya faru, jami’an kashe gobara sun gano wasu mutum hudu a sume, inda suka yi nasarar ceto wasu shida ciki har da direban bas din.

Advertisement

“Nan take an ba wa wadanda suka jikkata kulawa a kai asibitin NYSC na Takai, amma daga baya likitoci sun tabbatar da mutuwar mutum hudu,” in ji shi

Kakakin hukumar, ya gargadi masu ababen hawa da su rika tabbatar da ki’yaye ka’idojin tuki domin kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.

Advertisement

A wani labarin kuma Tsige Gwamnan Filato: Shari’a ta Zama Akwatin Gawar Dimokradiyya a Najeriya  – Shehu Sani

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending