Connect with us

News

Dalilin Gurfanar Da Muhuyi Magaji A Gaban Kotu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Hukumar da’ar ma’aikata ta bayyana dalilin da ya sa ta gurfanar da shugaban hukumar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji a gaban kuliya.

An gurfanar da Magaji a gaban kotun (CCT) bisa zargin cin hanci da rashawa 10.

Nadin Da Aka Yi Wa Alkalai 22 Na Kotun Koli A Najeriya Ya Tayar Da Kura A Bangaren Shari’a

An tattaro cewa Magaji zai bayyana a kotu a ranar 10 ga Janairu, 2024.

Manema labarai sun tattaro cewa an gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci na jihar Kano a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, a kotun CCT.

Advertisement

A cewar shugabar, manema labarai da hulda da jama’a, Misis Veronica Kato, tace tuhumar da ake yiwa Muhuyi Magaji ta hada da saba ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, cin zarafin ofishi, bayyana kadarorin karya, cin hanci, karbar kyauta, da sauransu.

Bincike ya nuna cewa shugaban ya gaza kare wasu asusu na banki masu dauke da sunansa mai dauke da kudi naira miliyan 394 wanda hakan ya sa ake masa zargin almundahana.

Ta ce, duk da haka an bayar da belin wanda ake tuhuma da kudi Naira miliyan 5 tare da mutane biyu masu tsaya masa da suke da kadarori a cikin babban birnin tarayya Abuja.

A wani labarin kuma Nadin Da Aka Yi Wa Alkalai 22 Na Kotun Koli A Najeriya Ya Tayar Da Kura A Bangaren Shari’a

Fitacciyar mawakiyar Colombia, Shakira ta cimma yarjejeniya da masu shigar da kara na kasar Sifaniya domin sasantawa kan tuhumar almundahanar biyan haraji, a daidai lokacin da ake shirin fara shari’arta.

Mawakiyar ta biya tarar Yuro miliyan 7.5m – masu gabatar da ƙara sun so a daure ta tsawon shekara takwas, sannan a ci tarar ta Yuro miliyan 23.8, idan aka same ta da laifi.

Advertisement

Ta fuskanci zargin almundahana a kan kuɗi Yuro miliyan 14.5 a wata kotun Barcelona.

Shakira, wadda ta sha musanta aikata wani laifi, ta ce ta cimma yarjejeniyar ne saboda da ƴaƴanta.

A cikin wani dogon bayani, ta ce ‘ya’yanta “ba sa son ganin mahaifiyarsu ta sadaukar da rayuwarta a kan wannan rikici”.

A baya dai, mawaƙiyar ta yi watsi da yarjejeniyar da masu gabatar da kara suka gabatar, a maimakon haka ta zaɓi zuwa kotu.

Rikicin ya shafi kasar da take zaune a ciki a tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2014, inda masu gabatar da kara suka ce ta zauna a Sifaniya amma ta lissafa zaman a wani wuri.

A karkashin dokar Sifaniya, mutanen da suka shafe fiye da wata shida a kasar, ana daukar su a matsayin mazauna ne ta fuskar dalilai na biyan haraji. Amma Shakira ta ce Sifaniya, ba ta kasance inda ta fi zama a lokacin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending