Connect with us

News

Nadin Da Aka Yi Wa Alkalai 22 Na Kotun Koli A Najeriya Ya Tayar Da Kura A Bangaren Shari’a

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Hakan ya faru ne saboda wasu manyan alkalai masu rike da mukaman gwamnati da wadanda suka yi ritaya sun shiga cikin jerin sunayen da hukumar kula da harkokin shari’a ta tarayya, ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Wani babban mai shari’a ya shaida wa manema labarai cewa, shugaban kasa Bola Tinubu zai iya fuskantar arangama kai tsaye da wani bangare na manyan ‘yan majalisar dokokin kasa,

Kwankwaso da gwamnan Kano sun jagoranci wani taron masu ruwa da tsaki bayan hukuncin Kotu

yana mai cewa “a tarihin Najeriya ba a taba nada alkalan kotun koli da aka sanya siyasa a ciki ba.

Wani mai shari’a kuma ya ce shari’ar shiyyar Arewa ta tsakiya inda aka sanya dan tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, a matsayin fifiko yayin da wani babban malamin shari’a wanda ya haura shekaru 15 a kotun daukaka kara, aka sanya shi a matsayin a jiya.

Advertisement

A wani labarin kuma Kwankwaso da gwamnan Kano sun jagoranci wani taron masu ruwa da tsaki bayan hukuncin Kotu

Rundunar ƴan sanda a Najeriya ta ce za ta ɗauki tsattsauran mataki kan duk wanda ya yi yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan hukuncin da kotu ta yanke kan shari’ar zaɓen gwamnan jihar.

 

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ƴan sandar ta fitar yau Litinin ta hannun mai magana da yawunta a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Sanar ta ce ta yi gargaɗin ne “bayan samun wasu bayanai da ke nuna cewa akwai wasu ƙungiyoyin magoya bayan wasu jam’iyyu da ke yunƙurin shirya zanga-zanga kan titunan birnin (Kano) domin nuna ɓacin rai kan hukuncin kotun ƙoli game da zaɓen gwamnan jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa “bayanai sun ce waɗanda ke shirya zanga-zangar na so ne su dakatar da harkokin a jihar ta Kano wanda hakan zai iya tayar da zaune tsaye.”

Advertisement

A ranar Juma’a da ta gabata ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta bai wa Nasiru Yusuf Gawuna nasara a zaɓen gwamnan jiha ta Kano, inda ta soke nasarar gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf.

Hukuncin kotun ya ce Abba bai cancanci zama ɗan takarar gwamna ba saboda rashin cika wasu ƙa’idoji.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending