Connect with us

News

Kiri-ƙiri alƙalai suke yi wa APC aiki a shari’o’in zaben Najeriya – Atiku Abubakar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Jagoran adawa a Najeriya ya yi zargin cewa manufar jam’iyya mai mulkin kasar wato APC, ta kwacen mulkin jam’iyyun adawa, babban naƙasu ne ga tsarin dimokraɗiyya.

Atiku Abubakar ya ce abin takaici ne yadda kwatsam suke ganin wani salo, inda jam’iyya mai mulki ke ci gaba da dakushe ƙoƙarin damawa da jam’iyyun adawa a harkokin mulkin Najeriya.

Joe Biden Ya Ce An Kusa ƙulla Yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas

“Ko dai ta hanyar zabe, inda ake yi wa jam’iyyun adawa maguɗi ƙuru-ƙuru cike da galatsi, ko kuma a kotuna inda ɓangaren shari’a ke yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki,” in ji shi.

“A bayyane take dimokradiyyar Najeriya tana ƙara shiga halin rashin lafiya.”

Sai dai wani alkali a daya daga cikin hukunce-hukuncen da aka yanke wadanda ba su yi wa ‘yan adawa dadi ba, ya zargi jam’iyyu da sakaci da kuma ƙin aiki da doka wajen fitar da ‘yan takara a zabukansu na fitar da gwani, daga bisani kuma su je suna zargin kotuna da alkalai da rashin adalci.

Advertisement

Atiku ya ce “azancin mulkin dimokradiyya bai tsaya kawai a kan gwamnati mai wakilcin jama’a ba kawai, ginshikinta ya samo asali ne daga akidun jam’un mutane”.

A cewarsa, kafin duk wani tsari ya amsa sunan dimokradiyya ta gaskiya, jazaman ne sai an shigar da ‘yan adawa da kuma ra’ayoyin ‘yan adawa.

A wani labarin kuma Joe Biden Ya Ce An Kusa ƙulla Yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ce aƙalla Falasɗinawa 13,300 aka kashe sakamakon hare-haren da Isra’ila take kaiwa tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Isra’ila ta fara kai hare-haren tun bayan harin da mayaƙan Hamas suka kai mata, inda suka kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu sama da 200 a ranar 7 ga watan.

Aƙalla yara 5,600 ne cikin waɗanda Isra’ilar ta kashe, da kuma mata 3,550 zuwa yanzu, in ji ma’aikatar lafiyar da Hamas ke gudanarwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending