Connect with us

News

Kotu ta bada dama Ajaka da SDP su binciki kayayyakin zaɓen Kogi

Published

on

DAGA. MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Kotun shigar da korafin zaɓe ta Tribunal da ke zamanta a Lakoja ta amince da bukatar ɗan takarar gwamna, Murtala Ajaka na SDP na a ba su damar binciken kayayyaki da takardun zaɓen da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Mai shari’a Yusuf Ado Birnin-Kudu da ya bada wannan umarni, ya umarci hukumar zaɓe ta INEC ta bada wannan dama a cikin sa’o’i 24.

Advertisement

Kotu ta yan kewa mai yin lalata da almajirai ta dubura hukuncin ɗaurin rai da rai

Wannan umarni na zuwa ne bayan da lauyan masu korafi ya ce duk wani kokarinsu na samun damar nazartar kayayyakin zaɓen a Abuja da Lakoja ya gaggara.

Sai dai Mai shari’a Birnin-Kudu ya ce dole ne a bada wannan dama bisa tanadi na dokokin zaɓe da aka yiwa gyaran fuska a 2023.

Advertisement

Hukumar zaɓe ta INEC dai ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kogin.

Ododo ya samu ƙuri’a 446,237, inda ya doke mai biye masa, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP, wanda ya samu ƙuri’u 259,052.

Advertisement

Dino Melaye na PDP ne ya zo na uku, inda ya samu ƙuri’u 46,362.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending