News
Yadda Hakimai 3 Suka Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Oyo
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Al’ummar Masarautar Ogbomoso a Jihar Oyo sun kidime da juyayi da rasuwar manyan hakimai uku a hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin Arinkinkin da ke Karamar Hukumar Orire.
Hakiman da suka rasu a ranar Juma’a sun hada da Olodogbo na Odogbo da Onibowula na Bowula da kuma Alayetoro na Ayetoro.
Wata majiya mai tushe ta ce, sarakunan da suke cikin mota daya suna kan hanyar zuwa jana’izar dan uwan wani takwaransu wato Oloolo na Oolo Oba Oyebunmi Ajayi ne a lokacin da hadarin ya auku.
Majiyar ta bayyana cewa, motar da suke ciki ce ta yi karo ne da wata babbar mota inda nan take suka rasa rayukansu.
Aminiya ta ruwaito cewa Mutum na hudu da ke cikin motar, wanda ake kyautata zaton direban motar ne ya samu raunuka da yanzu haka likitoci suke kokarin ceton ransa.
An kai gawarwarkin Asibitin koyarwa na LAUTECH da ke Ogbomoso.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
