Connect with us

News

Ƴan bindiga suka kashe mutum 9, suka yi garkuwa da mutane da dama a jihar Sokoto

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Akalla mutum tara suka mutu sannan aka yi garkuwa da mutane da dama a harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyuka uku a jihar Sokoto.

Maharan sun kai wa kauyen Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo, Chaco a karamar hukumar Wurno da Lambar Rabah dake karamar hukumar Rabah hari daga ranar Litini zuwa Talata.

Advertisement

Jami’yyar PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin Jihar Jigawa Bisa Cire Kudade Ba Bisa Ka’ida Ba

‘Yan bindigan sun kashe mutum 4 suka yi garkuwa da mutum 13 a kauyen Kojiyo. Sun kashe mutum uku a Lambar Raba, sannan da wasu mutum biyu. Sun yi garkuwa da wasu da dama a Rarba da wasu mutum 12 daga Chaco.

Premium Times ta ruwaito cewa Wani Ibrahim Halilu ya ce kanensa Hussaini Bello na daga cikin mutanen da maharan suka tafi da su daga kauyen.

Advertisement

A kauyen Lambar Rabah maharan a ranar Litini da safe sun kashe mutum uku kafin su zarce zuwa kauyen Kojiyo.

Wani mazaunin kauyen Lambar Rabah da baya so a fadi sunnan sa saboda yana aiki da gwamnatin jihar ya ce ga dukkan alamu maharan sun yi shirin afka wa kauyen Kojiyo hari ne amma da suka zo wucewa ta kauyen Lambar Rabah sai suka kashe mutum uku da sanyi safiya.

Advertisement

Mutumin ya ce maharan sun kashe mutum hudu sannan sun tafi da akalla mutum 13 a kauyen Kojiyo duk da kokarin da aka yi wajen fadakar da mutanen kauyen zuwan maharan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending