News
Gbajabiamila Ya Musanta Ware Masa Makudan Kudade Daga Cikin Kasafin Kudin Shekarar 2024
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ya musanta labarin da ake yadawa a yanar gizo cewa an ware masa makudan kudade daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin gyara gidan sa.
Ana ta rade-rade musamman a kafafen sada zumunta na zamani, kan cewa an ware kudi kimanin Bilyan 10 daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin shugaban ma’aikata na fadar shugaban ya gyara gidan sa, da kuma karin Naira Bilyan 10.1 domin siyan kayayyakin amfanin na’ura mai kwakwalwa.
Jami’yyar PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin Jihar Jigawa Bisa Cire Kudade Ba Bisa Ka’ida Ba
Shugaban ma’aikatar na fadar shugaban kasa yace ba’a ware masa komai ba daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin ya gyra gidan sa, inda yace yana zaune ne a gidan sa na kashin kan sa.
Ya bayyana cewa kudaden da aka Ambato an ware su ne domin gyra gidan fadar shugaban kasa da mataimakin sa dake Barikin Dodan a Jihar Legas.
Tsohon kakakin majalisar wakilan ya kara da cewa daga cikin abubuwan da za’a gyra akwai sashen sadarwa na zamani na fadar shugaban kasa, da kuma ababan hawa na fadar shugaban kasar.
A wani labarin kuma Jami’yyar PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin Jihar Jigawa Bisa Cire Kudade Ba Bisa Ka’ida Ba
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
