Connect with us

News

Daliban Jami’ar Da Aka Sace A Nasarawa Sun Kubuta

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Dalibai takwas da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga Jami’ar Tarayya ta Lafia da ke Jihar Nasarawa sun kubuta.

A ranar 6 ga wata ne ’yan bindiga suka kutsa unguwar Gandu da ke Lafia suka yi awon gaba da daliban, daga dakunan kwanansu a unguwar.

Kungiyar AROGMA Ta Bukaci Majalisar Dattijai Ta Binciki Yadda NIPCO Ta Murkushe Hannun Jarin Dillalan Man Fetur

Wani shugaban al’umma a yankin Keana, Spencer Jerry, ya ce ɗaliban sun iso yankin Kwarra a ranar Lahadi da dare, daga nan aka kai su wurin jami’an tsaro.

Hakimin Gandu, Abdullahi Mohammed ya ce an kai ɗaliban asibitin da ke cikin jami’ar domin duba lafiyarsu.

Amma jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar cewa an sako su da misalin karfe 8 na ranar Lahadi, kuma ana duba lafiyarsu.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Jami’in ya ce hukumar jami’ar da gwamnatin jihar sun hada kai wajen tsaurara matakan tsaro domin hana aukuwar irin haka a nan gaba.

Ya kuma bukaci gwamnatin jihar ta yi cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya fari

Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar Nasarawa DSP Rahman Nansel domin samun karin haske a kan lamarin.

A wani labarin kuma Kungiyar AROGMA Ta Bukaci Majalisar Dattijai Ta Binciki Yadda NIPCO Ta Murkushe Hannun Jarin Dillalan Man Fetur

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending