News
Harajin da ake karɓa daga kamfanoni ya ƙaru da kashi 116% – Hukumar NBS
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, wato NBS ta ce kamfani sun biya Gwamnatin Tarayya harajin Naira tiriliyan 1.74 a matsayin kuɗaɗen haraji na watannin Yuli, Agusta da Oktoba.
Hukumar ta yi wannan bayanin a ranar Litinin. Saboda haka idan aka kwatanta da abin da aka tara watannin Yuli, Agusta da Satumban 2022, za a ga cewa harajin ya ƙaru da kashi 115.9 kenan.
Hatsarin Jirgin Kwale-Kwale Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Jihar Adamawa
Premium Times ta ruwaito cewa watannin Yuli, Agusta da Satumba na Shekarar 2023 an samu ƙarin idan aka kwanta da naira tiriliyan 1.53 da aka tara a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na shekarar 2023.
Rahoton ya ce harajin da aka tara Naira biliyan 652.83 ne, sai kuma Naira tiriliyan 1.10 a watannin Yuli, Agusta da Satumba na 2023.
Masu lura da al’amurran yau da kullum da kuma tattalin arzikin ƙasa na ganin cewa haraji da sauran matsalolin da suka addabi tattalin arzikin ƙasar nan na daga cikin dalilan da suka sa wasu manyan kamfanonin Turai da ke ƙasar nan za su daina sarrafa kaya a ƙasar nan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu masana’antu da dama za su rufe su kwashe komatsan su su fice daga ƙasar.
Sun buga misali da matsalar yawan haraji, matsalar tsaro, rashin wutar lantarki da kuma babbar matsala wato tashin gwauron zabo da dala ke yi a kullum, a gefe guda kuma darajar naira a kulum sai zubewa take yi.
Yawancin kayan da masana’antun ke sarrafawa dai duk daga waje suke shigo da su.
A wani labarin kuma Hatsarin Jirgin Kwale-Kwale Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Jihar Adamawa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
