News
Hatsarin Jirgin Kwale-Kwale Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Jihar Adamawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar wata ma’aikaciyar jinya da ‘yarta, sakamakon hatsarin jirgin ruwa a garin Gamadio da ke karamar hukumar Numan a Jihar Adamawa.
Shugaban karamar hukumar Numan, Honarabul Christopher Sofore, ya bayyana haka ga tawagar gwamnatin jihar da mataimakiyar gwamna Farfesa, Kaletapwa George Farauta, ta jagoranta, zuwa garin a ranar Litinin.
Alƙalin wasa ya sha naushi daga shugaban wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa
Ya ci gaba da cewa “mutum biyar ke cikin jirgin ruwan lokacin da hatsarin ya faru, an yi nasarar kubutar da mutum uku, amma mutum biyu, jami’an NEMA sun tabbatar da mutuwarsu” inji Sofore.
Leadership ta ruwaito cewa Da ta ke maida martani,vmataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta kalubalanci hukumomin bada agajin da su tilasta amfani da rigar-Kariya (life jacket), da cewa zai takaita rasa rayuka da dukiyoyin ake Koda hadarin ya auku.
Ta ci gaba da cewa “dole mu dauki matakan kare rayukan jama’a, shugabannin kananan hukumomi, su tabbatar Rigar-Kariya (life jacket), ta wadata a yankunan kananan hukumomin da ake samun matsalar hatsarin ruwa” in ji Farauta.
Mataimakiyar gwamnan ta kuma jajanta wa iyalai da jama’ar yankin Gamadio, game da rashin, ta kuma karfafa batun amfani da Rigar kariya duk lokacin da jama’a za su shiga jirgin ruwa.
A wani labarin kuma Alƙalin wasa ya sha naushi daga shugaban wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
