Connect with us

News

Kungiyoyin Kwadago Sunce Gwamnatin Tarayya Ta Yaudare Su Kan Karin Albashi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Gamaiyyar kungiyoyin kwadago a kasar nan sunga baiken gwamnatin tarayya kan rashin cigaba a biyan ma’aikata karin albashi na wucin gadi na naira dubu 35 da aka yi masu, sakamakon janye tallafin mai da aka yi.

A jiya ne ma’aikatan gwamnatin tarayya suka tabbatar da cewar, gwamnatin ta yi masu karin naira dubu 35 ne sau daya kadai a albashinsu na watan Satumba, sabanin alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi, na cewar za’a cigaba da basu karin har zuwa lokacin za’a bullo da sabon tsarin biyan albashi mafi kankanta.

Tudun Biri: Tawagar ‘Yan Majalisar Wakilai Na Arewa Ta Bayar Da Gudunmuwar Naira Miliyan N350m

Shugaban sashin yada labarai na kungiyar kwadago ta kasa, Benson Upah ya baiyana matakin a matsayin na yaudara wanda kuma ba zasu lamunta ba, inda y ace kungiyar zata dauki mataki batare da bata lokaci ba.

To sai dai kakakin ofishin babban akanta na kasa, Bawa Mokwa ya kawar da fargabar da ma’aikatan suka nuna, inda ya ce a yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin tabbatar da ma’aikatan sun karbi karbin albashin na wucin gadi da aka yi masu.

Advertisement

A wani labarin kuma Tudun Biri: Tawagar ‘Yan Majalisar Wakilai Na Arewa Ta Bayar Da Gudunmuwar Naira Miliyan N350m

Wani lauya na musamman ya nemi Kotun Kolin Amurka ta yanke hukunci a kan ikirarin ko ana iya gurfanar da tsohon shugaban kasar Donald Trump a gaban kotu kan zargin shirya makarkashiya don tafka magudin zaben 2020.

Lauya Jack Smith na son kotun kolin ta yanke hukuncin cikin sauri a kan ikirarin Donald Trump na cewa yana da rigar kariyar shugaban kasa.

Rokon ya zo ne bayan Mista Trump ya nemi a jinkirta shari’arsa a daidai lokacin da kotunan daukaka kara ke sauraron kararrakin da aka gabatar.

A yanzu haka dai an tsara cewa za a fara sauraron shari’ar ranar 4 ga watan Maris a Washington DC.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending