Connect with us

Opinion

Har Yanzu Babu Wani Shugaba Da Ya magantu akan tsadar kayan masarufi najeriya – Honorable Baffa Gwarzo

Published

on

HON. MUHAMMAD YUSUF INUWA ( BAFFA GWARZO)

 

 

Advertisement

Tsadar kayan masarufi da kuma sauran kayan amfani ga al,umma ta addabi al, umma a wannan zamani kuma har yanzu babu wani mutum ko shugaba da ya taba yin magana a inda yakamata .

Haka kuma Malamam mu na addini da yawan sun ja bakin su sun yi shiru saboda kowa ba ya so ace yayi lefi, Allah ya jikan magabatan mu Allah ya kara jaddada Rahma a kabarin su (amin) a lokutan baya a duk sanda a ka tsinkai a wani irin yanayi malamam mu da sarakunan mu su ne su ke futowa su gayawa duk wadanda abun ya shafa gaskiya.

Advertisement

Kotun Koli ta Sanya Ranar sauraren karar Zaben Gwamnan Jihar Kano  

Idan kuma su kai maganar ba su dauka ba sai su koma su kai karar su waje Allah (S W T) domin shine sarkin da baya zalinci a mulkin sa bai haifa ba kuma ba a haife shi ba kuma baya gyangyadi a mulkin sa kuma maji rokon bayin sane idan mun roke shi to zai amsa ma na sai dan jin kiri domin shi baya gaggawa a mulkin sa.

Dan haka ina kira ga Yan uwa musulmai da mu dagye da addu,a akan wannan tsadar rayuwar da tai mana yawa har Allah ya kawo mana saukin ta sannan kuma muna rokon Allah akan duk wanda ya ke da sa hannu a wannan yanayi da a ka sa mu ko kuma yake da damar da zai hana bai hana ba.

Advertisement

Ya Allah kai mana maganin sa dan San da ka ke yiwa bawan ka masoyin ka kuma mafi girma a wajen ka wanda kace idan ya amsa toh angama Allah kai mana magani azzaliman nan kuma sanko mana da wadannan kayayyakin idan kuma sun sanko Allah ka hore al, ummar Annabi S A W abun da za suya.

Haka ma Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa ku a yau Hukumar Kididdiga Ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki sun kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da a ga hakan tun a shekarar 1996.

Advertisement

 

HON. MUHAMMAD YUSUF INUWA ( BAFFA GWARZO)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending