Connect with us

News

Cutar Bakon Dauro Ta Yi Ajalin Yara 190 A Najeriya Daga 2022 Zuwa Yanzu – Hukumar NCDC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa 2023 yara 303 sun kamu sannan cutar Bakon Dauro ta yi ajalin yara 190 a jihohi 29 da Abuja.

Advertisement

NCDC ta ce a tsakanin wannan lokacin an samu mutum 2,765 da suka kamu da cutar a kananan hukumomi 140 a jihohi 29 a faɗin kasar nan.

Rashin Ɗa Namiji Ya Sa Wata Matashiya Gadon Sana’ar Wanzanci A Jihar Kano

Hukumar ta ce cutar ta yaɗu a duka jihohin yankin Arewa, wasu jihohin Kudu da suka hada da Bayelsa, Cross River, Delta, Ekiti, Ogun, Ondo da Osun da Abuja.

Advertisement

Yara kanana masu shekaru 5 zuwa 14 na daga cikin yawan da suka fi kamuwa da cutar.

Hukumar ta ce ta hada hannu da ma’aikatar kiwon lafiya da inganta al’ummma domin daukan matakan da za a bi don dakile yaduwar cutar.

Advertisement

BAKON DAURO

Bakon dauro cuta ce da kwayoyin cutar ‘Virus’ ke haddasa ta sannan rashin daukan mataki game da cutar ne ke yin ajalin yara kanana.

Advertisement

Akan kamu da bakon dauro ta hanyar shakar kwayoyin wannan cuta ta iska, yin tari, yawan zama da mai dauke da cutar,sannan cutar kan dauki tsawon kwanaki 14 kafin ya nuna alamu.

Premium Times ta ruwaito cewar alamun bakon dauro sun hada da zazzabi,tari,mura, kurarraji, rashin iya cin abinci da sauran su.

Advertisement

Malaman asibiti sun yi kira ga mutane da su hanzarta zuwa asibiti idan aka ji ba daɗi a jiki.

Yi wa yara allurar rigakafi a lokacin da ya kamata na daga cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar bakon dauro da sauran su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending