Connect with us

News

Hukumar NAHCON ta tsayar da N4.8m a matsayin kudin Hajjin bana na 2024

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta kayyade Naira miliyan 4.8 a matsayin kudin aikin Hajjin shekarar 2024 ga maniyyatan da suka tashi daga Kudu.

Malam Jalal Arabi, Shugaban Hukumar NAHCON ne ya bayyana haka a wata sanarwa dauke da sa hannun Misis Fatima Sanda-Usara, mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta NAHCON a Abuja ranar Asabar.

Da dumi dumi Gwamnan babbaan banki Hafize Gaye Erkan tayi murabus daga mukaminta

Ya ce hukumar ta samu rangwame mai yawa daga masu samar da hidima a kasar Saudiyya domin rage farashin maniyyatan da suke son zuwa aikin hajji.

Arabi ya ce kudin aikin Hajjin 2024 zai kai Naira miliyan 6 saboda tabarbarewar kudin Najeriya, amma ga hukumar ta sa baki ta hanyar karfafa nasarorin da aka samu wajen rage farashin ayyukan aikin hajjin bana.

Advertisement

“Saboda haka, ana bukatar maniyyatan da suka fito daga yankin Kudancin Najeriya su biya N4,899,000 a matsayin kudin aikin Hajji.

“Wadanda daga cibiyar Arewa za su biya Naira miliyan 4,699,000, na aikin Hajji, kuma mahajjata daga Yola da Maiduguri za su biya Naira miliyan 4,679,000 na aikin Hajjin 2024.

Arabi ya shawarci maniyyatan da su ke da niyyar daidaita kudin aikin Hajjin zuwa ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu domin baiwa hukumar damar mika kudaden kafin cikar wa’adin.

Ya kuma ba da tabbacin hukumar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara  dukkan maniyyatan da ke da niyyar zuwa aikin Hajji duk da kalubalen da ke tattare da canjin kudaden kasashen waje.

“Hukumar ta yaba da fahimta da hadin kan al’ummar Musulmin Najeriya a wadannan lokutan,” inji shi.

 

Advertisement

Prime Time 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending