Connect with us

News

Da dumi dumi Gwamnan babbaan banki Hafize Gaye Erkan tayi murabus daga mukaminta

Published

on

Gwamnan babban bankin Turkiyya Hafize Gaye

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hafize Gaye Erkan Gwamnan babban bankin Tukiya da ta shafe kasa da shekara guda a wannan mukami ta sanar da yin murabus a jiya Juma’a a kamar yada ta wallafa a shafukan sada zumunta, sakamakon wata badakala da ta shafi ‘yan uwanta.

Advertisement

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya maye gurbinta da mataimakinta,tsohon masanin tattalin arzikin Amazon Fatih Karahan, wanda aka haifa a shekarar 1982.

 

Advertisement

Fatih Karahan ya fara aikin a matsayin masanin tattalin arziki a babban bankin tarayya na New York na kasar Amurka a shekarar 2012.

 

Advertisement

Ya koma Amazon a shekarar 2022, da kuma babban bankin Turkiya a watan yulin shekarar 2023.

 

Advertisement

Yan lokuta da sauka daga wannan mukami daga uwargida Hafize Gaye Erkan, Shugaban kasar Erdogan ya tabbatar da Fatih Karahan, a wani lokaci a can baya da kasar ta yi fama da matsalollin tattalin arziki.

 

Advertisement

Kafofin yada labaran Turkiya da dama na zargin Hafize Gaye Erkan da laifin baiwa danginta dama a babban bankin kasar, lamarin da ta musanta

.

Advertisement

Hafize Gaye Erkan, tsofuwar Gwamnan mai shekaru 44 da haihuwa, mace ta farko a wannan matsayi kuma ta yi fice saboda kwarewarta a Amurka, ta fara aiki ne a farkon watan Yuni bayan sake zaben shugaba Erdogan.

 

Advertisement

Ana zarginta da laifin barin mahaifinta ya yanke hukunci ba bisa ka’ida ba a babban bankin kasar

.

Advertisement

A cewar masu lura da al’amuran yau da kullun, ta fuskanci fushin shugaban ne a lokacin da ta shaida wa wata jaridar kasar Turkiya a watan Disamba cewa an tilasta mata komawa zama da iyayenta, tare da ‘ya’yanta da mijinta, saboda hauhawar farashin kayayyaki da wasu dalilai daban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending