News
Sake zaben Kano: An tsaurara matakan tsaro a rumfunan zabe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An tanadi jami’an tsaro a dukkan rumfunan zabe da ke gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da ke ci gaba da gudana.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa ana sake gudanar da zaben ne a mazabu uku: Tsanyawa/Kunchi, Kura/Garun Mallam da Tofa/Rimin Gado.
Yadda ‘Yan Bindiga Suka Sace Mahalarta Ɗaurin Aure 55, Da Kashe Mutane 3
Wakilin PUNCH da ya ziyarci karamar hukumar Kura ya ruwaito cewa an samar da isassun jami’an tsaro a rumfunan zabe yayin da masu kada kuri’a ke kada kuri’a ba tare da wani shamaki ba.
Tun da farko kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya gargadi masu tayar da zaune tsaye da su guji shiga wuraren da za a sake gudanar da zabe.
Bugu da kari, ba za a amince da daukar duk wani nau’in makamai a yayin sake zaben ba, domin wadanda suka cancanci kada kuri’a da INEC za ta tantance ne kadai za su kada kuri’a.
Hakazalika, jami’an tsaro a wuraren da aka gudanar da zabukan sun yi wa masu kada kuri’a cikakken bincike don tabbatar da zaman lafiya a wuraren zaben.
Haka labarin yake a mazabar Tafasa da ke karkashin gundumar Kurunsumau. Ana kuma sake gudanar da zaben a yankunan Kosawa da Danhassan.
Rahotanni daga sauran kananan hukumomin da abin ya shafa sun nuna cewa zaben yana gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba.
