News
Sai da aka sace ni na fara goyon bayan biyan kuɗin fansa – Tsohon daraktan DSS
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mista Mike Ejiofor, ya bayyana cewa, tunaninsa na ƙin biyan kuɗin fansa na garkuwa da mutane ya canja bayan da a ka sace shi da kansa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ya yi watsi da batun biyan kuɗin fansa, ya jaddada cewa taɓarɓarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar nan na sa mutane shiga harkar garkuwa da mutane a matsayin wata hanyar samun kuɗin shiga.
Ejiofor ya amince da damuwar da ake samu game da ƙaruwar satar mutane tare da jaddada buƙatar samar da hanyoyin da za a bi don magance matsalar.
Ya ba da shawarar cewa ba lallai a kau da matsalar bakiɗaya ba, amma tana buqatar a tura isassun kayan aiki, tare da mai da hankali kan sa ido sosai don tabbatar da an yi amfani da kuɗaɗen da aka ware domin tsaro yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana muhimmancin hana almubazzaranci da salon rayuwa a tsakanin shugabannin hukumomin tsaro, inda ya nuna cewa ya kamata a karkatar da kuɗaɗen wajen magance matsalolin rashin tsaro a maimakon son kai.
Ejiofor ya kammala da cewa, tavarvarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar nan na taimakawa wajen yawaitar garkuwa da mutane kamar yadda daidaikun mutane ke ɗauka a matsayin sana’ar samun riba a cikin wahalhalun da ake fama da su.
Ya jaddada gaggawar magance ƙalubalen tattalin arziki a matsayin wani vangare na hanyoyin da za a magance ayyukan aikata laifuka.