Connect with us

News

Hukumar INEC ta kashe Naira biliyan 313.4 wajen shirya zaɓen Shakarar 2023 – Rahoto

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Rahoton ayyukan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gudanar cikin shekarar 2023, ya tabbatar da cewa an kashe Naira biliyan 313.4 wajen shirya zaɓukan 2023.

Hukumar ta ce ta nemi Gwamnatin Tarayya ta ba ta Naira biliyan 355, amma zuwa watan Satumba, 2023 dai ta karbi Naira biliyan 313.4. Haka dai rahoton wanda aka fitar ranar Juma’a ya ce tabbatar.

Advertisement

Yan Sanda Zasu Bada Isasshen Tsaro A Matsugunin Dillalan Magunguna Dake Dan Gwauro  – CP   

Rahoton ya ci gaba da cewa INEC ta yi kasafin Naira biliyan 305 domin shirya zaɓe tun da farko.

An kashe Naira biliyan 159.7 wajen gudanar da ayyukan zaɓe; an kashe Naira biliyan 117.3 wajen sayen kayayyaki da na’urorin fasaha; an kashe Naira biliyan 20.4 wajen tafiyar da ayyukan yau da kullum a ofisoshin hukumar zaɓe.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa rahoton ya nuna an kashe Naira biliyan 7.4 wajen ayyukan zaɓe wajen wasu matsalolin da ka je su taso daga baya.

“Majalisar Tarayya ta amince a kashe Naira biliyan 303.1 wajen gudanar da zaɓen 2023. Amma kuma daga baya a cikin watan Janairu sai ya kasance kuɗaɗen ba za su isa ba.

Advertisement

Rahoton ya bayyana irin wurare da ofisoshin INEC da aka banka wa wuta ko aka lalata, waɗanda tilas suna buƙatar gyara kafin zaɓe, a sama da hare-hare 50 da ta ce an kai tsakanin 2019 da 2022.”

Ta ce hakan ne ya sa tilas ta nemi ƙarin kuɗaɗen daga baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending