News
Yan Sanda Zasu Bada Isasshen Tsaro A Matsugunin Dillalan Magunguna Dake Dan Gwauro – CP
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce za ta samar da isasshen tsaro ga ‘yan kasuwar sayar da magunguna na kasuwar Sabon Gari da ke shirin komawa sabuwar Dan Gwauro dake Jihar Kano
Rundunar ta ce za ta tabbatar da tsaron ‘yan kasuwar a lokacin da suke jigilar kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwar.
Mun gaji da irin wulakancin da akewa yan Nigeria cewar majalissar Wakilan
Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel ne ya bayar da wannan tabbacin a wata hira da manema labarai a Kano ranar Lahadi.
Gumel ya ce rundunar ta tanadi matakan tsaro da za su baiwa ‘yan kasuwa damar jigilar kayayyakinsu cikin kwanciyar hankali.
Don haka, ya ce an ba Kwamandan yankin da jami’an ‘yan sanda shiyya (DPOs) a kananan hukumomin Fagge da Kumbosto da ke jihar Oda mai aiki da takamaiman aiki.
Ya ce matakan tsaro za su hana ’yan daba yin wawashe shagunan ‘yan kasuwa da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin da ake gudanar da aikin sake tsugunar da su.
“Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro a dukkan hanyoyin da za su bi zuwa sabuwar kasuwar magunguna da aka kafa a Dangwauro a karamar hukumar Kumbosto.
“Ina ba da tabbacin kashi 100 ga duk ‘yan kasuwa masu bin doka da oda na jihar su je su yi jigilar kayansu cikin walwala ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji Kwamishinan.
