News
Umarnin Shigo Da Kayan Masarufi Daga Kasar Waje Shine Abunda Al’ummar Najeriya Ke Buƙata Sama Da Komai A Halin Yanz —Gamaiyar Kungiyoyi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu na arewacin najeriya ciki har da babban birnin tarayya Abuja Amb. Ibrahim Waiya ya umarnin shigo da kayan masarufi daga iyakokin kasar Najeriya shine abunda al’ummar Najeriya ke buƙata sama da komai a halin yanzu.
Hakan na kunshe ne ta cikin takardar manema labarai da ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bashir A Bashir ya turawa da Jaridar Inda Ranka
Abdul Ningi na da gaskiya, ƙadan ma ya bankaɗo, akwai da yawa binne a Kasafin
Amb. Waiya yace shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bada dama a shigo da kayan abinci domin shine hanya ɗaya tilo da al’ummar Najeriya zai samu sassauci a yanayin da ake ciki na halin yunwa da sauran sace-sace da ake fama dashi na dalibai a kasar nan.
Har yanzu shugabannin Najeriya suna amfani ne da shinkafar ƙasar waje a gidajen su amma sun hana talakan kasa samun ta waje sun ce sai dai ya noma yaci.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
