News
Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan goma 15.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wani mataki na rage radadin talauci a tsakanin al’umma, gidauniyyar Dangote ta kaddamar da tallafin rabon abinci na kasa a jihohin kasar nan inda mutane miliyan daya suka amfana.
Jihar Kano ta samu kaso mafi girma inda mutane 120,000 suka amfana wanda daga bi sani rabon zai ci gaba a sauran jihohin kasar nan.
Haka zalika rabon shinkafa mai kilo 10 zai ci gaba a dukkanin sauran kananan hukumomi na Jihar Kano.
Bikin kaddamar da rabon abincin dai ya gudana ne a budadden dakin taro na fadar Gwamnatin Kano da shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta da kuma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
A cewar Alhaji Aliko Dangote , sun ga dacewar raba kayan abincin ne ba wai kawai don magance matsalar yunwa ba, har da batun saukakawa al’umma wajen gudanar da rayuwa a kasa ba-ki daya.
“Hakan kuwa ya zama wajibi duba da muhimmancin zumunci da ‘yan uwan taka dake tsakanin mu, da kuma hadin kai a wannan lokaci da ake fusakantar kalubalen rayuwa.
“A wannan wata na Ramadan, lokaci ne da muke sadar da halayen nagarta, wanda ke taimakawa wajen tallafawa al’umma”.
Alhaji Aliko Dangote ya nanata cewa tallafin zai game dukkanin kananan hukumomin kasar nan 774, na kimanin buhunan shinkafa milyan daya inda Kano zata samu kaso mai tsoka na buhuna 120,000.
“Ina da kwarin gwuiwar sanar daku cewa wannan tallafin na yanzu na musamman ne, duk da cewar mun yi irin sa a kasa da wata guda da ya gabata, amman muka ga dacewar sake tallafawa al’umma musamman a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.
Attajirin Alhaji Aliko Dangote, ya shaidawa gangamin taron al’ummar cewa wannan kari ne akan tallafin da ya gudana na mutane dubu goma da ake ciyarwa kullum a Jihar Kano, yace Tallafin shinksfar Mai kilo goma da ya kaddamar kimanin miliyan Daya wanda ya lakume kudade bilyan 15 a kasa ba-ki daya.
Da yake jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shirin rabon tallafin kayan abincin inda yace yazo a dai-dai lokacin da dimbin al’umma ke bukatar hakan.
Gwamnan ya bukaci kwamitin da aka dorawa nauyin rabon kayan abincin ciki har da hukumar HISBAH ta jiha da su maida hankali wajen aiwatar da aikin cikin gaskiya da rikon amana don cimma manufar shirin.
“Wannan shirin zai taimaka wajen rage saukaka rayuwa, a cewar Gwamnan Kano.
“Inda ya sake kara jinjina kaso mafi tsoka da jihar ta samu”.
Zouera Yousoufou dake zaman shugaban gidauniyyar ta Aliko Dangote tayi karin haske kan kokarin Alhaji Aliko Dangote wajen tallafawa al’umma, inda yace shakka babu gidauniyyar zata ci gaba da baiwa wannan bangaren muhimmanci.
“Mune a gidauniyyar Dangote muke ganin ya zama wajibi a sanar da al’umma irin kokarin da yake yi don sauran al’umma masu kudi su kwaikwayi halayensa na gari na tallafawa al’umma”, a cewar Yousoufou.
Rabon tallafin kayan abincin da Alhaji Aliko Dangote ya jagoranta na shinkafa miliyan Daya dake dauke da kilo goma na nuni da kokarin shi wajen rage radadin rayuwa da marasa galihu ke fuskanta da kuma kara dankon zumunci a tsakanin al’umma.