Connect with us

News

Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi

Published

on

DAGA YADIR SANI ABDULLAHI 

Dan Takarar Shugabancin Najeriya na Jam’iyyar LP a Zaben 2023 ya bayyana cewa riƙe  harkar noma ce kaɗai hanyar magance rashin tsaro, yunwa, fatara da talauci a Najeriya.

Advertisement

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Birnin Kebbi yayin ci gaba da zagayen buɗa baki da ya ke yi a jihohin Najeriya.

Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan goma 15.

Ya ce, “a duniya Najeriya ce kasar da ta fi yawan gonakin da ba a nomawa, kuma abin mamaki da yawansu a Arewacin Najeriya su ke.”

Advertisement

Obi ya ce da za a maida hankali kan noma to da an yi sallama da matsalar tsaro da talauci a Najeriya.

Ya kara da cewa “zuwansa Kebbi ya ciyar da masu azumi ɗari, ya kuma ƙaddamar da rijiyar burtsatsai mai amfani da hasken rana a Hutawa wani kauyen Fulani a Birnin Kebbi.”

Advertisement

Da ya ke jawabi ga Peter Obi, Gwamnan Jihar Kebbi da Sakatarensa Alhaji Yakubu Bala-Tafida ya wakilta ya ce, “gaskiya ne abin da Obi ya faɗi, shi yasa suka fara saka dan ba wurin tallafin noma ga al’ummar jihar”.

Tafida ya kuma yi godiya ga tsohon Gwamnan na Jihar Anambra kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Advertisement

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsu ta sayi taki na Naira Biliyan 2.9 ta raba wa al’ummar jihar, ba tare da la’akari da jam’iyyar da mutum ya fito ba.

Aminiya ta ruwaito cewa ya ce “mun samar da injinan ban ruwa da sauran kayayyakin aikin gona ga dubban mutane a Jihar.”

Advertisement

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce, babban makasudin da ya sa take wannan yunƙuri shi ne su saukaka wa manoma hanyar aikinsu.

Ya ƙara da cewa, hakan zai taimaka wajen samar da abinci mai rahusa ga jama’ar jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending