News
Peter Obi Ya Danganta Talaucin Najeriya Da Rashin Nagartaccen Shugabanci
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa matsalar talauci da Najeriya ke fama da ita ba ta samo asali daga rashin albarkatun ƙasa ba, sai dai daga zabukan shugabanci da ƙasar ke yi.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a birnin Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar ƙwararrun ma’aikata da masu sana’o’in hannu ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Obijuru Everest.
Jami’an Tsaro Sun Dakile Wani Yunƙurin Garkuwa Da Mutane A Kano
A cewarsa, Najeriya ƙasa ce da Allah Ya albarkace ta da dimbin arzikin ƙasa da kuma yawan jama’a, wanda ya kamata hakan ya zama ginshiƙi na bunƙasar tattalin arziƙi.
Sai dai ya ce duk da irin wadannan albarkatu, har yanzu ƙasar na fama da matsalolin talauci da koma baya, abin da ya danganta da matsalolin shugabanci.
Peter Obi ya ce daya daga cikin manyan matsalolin da ke janyo koma bayan Najeriya shi ne al’adar da ake yi na girmama cin hanci da rashawa maimakon a yaƙe ta.
Ya kuma kwatanta Najeriya da ƙasar Indonesia, wadda ya ce tana da yawan jama’a kusan daidai da Najeriya, amma ta samu ci gaba mai kyau a fannin tattalin arziƙi sakamakon ingantaccen shugabanci da kuma sanya abubuwan da suka shafi ci gaba a gaba.
A cewarsa, ƙasashen da tattalin arziƙinsu ke bunƙasa cikin ɗorewa sukan mayar da hankali ne kan ci gaban jama’arsu da kuma tallafa wa ƙananan masana’antu.
Obi ya jaddada cewa ƙananan masana’antu ba za su bunƙasa ba sai idan gwamnati ta samar da tsari mai gaskiya da tabbas wanda ba shi da cikas ko rashin adalci.
