Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Sabbin Dakarun Soji 28,000 Cikin Shekara Guda 

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin sojoji sama da 28,000 tare da horas da su cikin shekara guda domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar.

Shaibu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, a birnin Makurdi. Ya ce shirin na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka domin ƙarfafa rundunar soji wajen tunkarar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Advertisement

Jami’an Tsaro Sun Dakile Wani Yunƙurin Garkuwa Da Mutane A Kano 

A cewarsa, baya ga shirin ƙara yawan sojoji, rundunar sojin ƙasar na kuma faɗaɗa dabarun yaki da rashin tsaro ta hanyar haɗa matakan soja (kinetic) da kuma matakan hulɗa da al’umma (non-kinetic) domin samun bayanan sirri da haɗin kan jama’a.

Advertisement

Babban hafsan sojin ya kuma bayyana cewa rundunar ta tura sabon bataliya zuwa ƙaramar hukumar Kwande a Jihar Benue domin ƙarfafa ayyukan tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin.

Haka kuma ya ce rundunar na shirin ƙara amfani da jirage masu saukar ungulu domin inganta saurin kai ɗauki a ayyukan tsaro, musamman a aikin Operation Whirl Stroke da ke yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin.

Advertisement

A nasa jawabin, gwamnan Jihar Benue Hyacinth Alia ya yabawa gwamnatin tarayya da rundunar sojin ƙasa kan haɗin gwiwar da suke yi wajen rage matsalolin tsaro a jihar. Ya ce haɗin gwiwar ya taimaka wajen rage yawan ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro daga 17 zuwa uku kacal.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa rundunar soji domin tabbatar da zaman lafiya a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending