Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Dakile Wani Yunƙurin Garkuwa Da Mutane A Kano 

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a Kano

Jami’an tsaro sun dakile wani yunƙurin garkuwa da mutane a ƙauyen Rantan da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji a Jihar Kano, inda suka ceto mutum biyu, yayin da wani ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar 2 ga watan Maris, 2026, bayan wani mazaunin yankin ya sanar da jami’an tsaro ta hanyar kiran gaggawa.

Advertisement

Amurka Ta Bukaci Ƙananan Jami’anta Su Fice Daga Yankin Gabas Ta Tsakiya

Wani masani kan al’amuran tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa kimanin wasu ‘yan bindiga 15 ne suka kai farmaki gidan wani da ake kira Fulani Bakwai, inda suka yi awon gaba da shi tare da maƙwabcinsa, Mohammed Bello.

Advertisement

Majiyar ta ce maharan sun harbi Musa Mohammed Bello, mai shekaru 25, a ƙafarsa ta hagu lokacin da ya yi ƙoƙarin hana su tafiya da waɗanda suka sace.

Sai dai bayan samun rahoto, jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai na yankin suka bi sawun maharan, lamarin da ya kai ga kuɓutar da mutanen biyu, yayin da maharan suka tsere zuwa cikin daji.

Advertisement

An kai wanda aka harba Asibitin Tiga domin ba shi kulawa, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa. An miƙa gawarsa ga iyalansa domin yi masa jana’iza.

Mahukunta sun ce an dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da ake ci gaba da farautar waɗanda suka tsere

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending