Connect with us

News

Kisan Soja 17 A Delta: Sojoji sun bankaɗo muggan makamai a gidan wani dillalin bindigogi

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

Sojojin Najeriya sun bayyana bankaɗo wani dillalin bindigogi, wanda aka samu muggan makamai a gidan sa da ke jihar Delta.

Advertisement

Cikin wata sanarwa da suka buga a shafin Facebook a ranar Alhamis, sun ce sojoji sun bankaɗo muggan makamai da albarusai a rumbun ajiyar muggan makamai da ke gidan sa a Olota da wasu ƙauyukan cikin Ƙaramar Hukumar Ughelli da ke cikin jihar.

Babbar Magana: Likitoci Sun Ciro Kifi Mai Rai Daga Cikin Wani

Sojojin Najeriya sun ce sun kai farmaki a ɗa dai rumbun bayan sun bi sawun wani da ake zargi, har suka riski inda ake ɓoye muggan makamai da dillalin ke safara, wanda ake kira da suna Mista Kenneth.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa an samu bindiga da albarusai 753 samfurin NATO, sai kuma guda 19 samfurin 7.62mm.

“Sojoji sun ci gaba da nausawa har cikin wasu yankuna, inda suka ƙara bankaɗo bindigogi 4 da jigida-jigidar albarusai, sai kuma bindiga ɗaya samfurin PA, sai wata mai bindiga ɗaya mai sarrafa kan ta, mashinga guda uku, wasu jigida-jigida da albarusai 476.”

Advertisement

Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce an kama mutum uku, amma ba a nuna hotunan su ba.

Sojoji sun ce wannan farmakin su na yi ne domin kakkaɓe haramtattun makamai daga yankin na Kudu maso Kudu.

Advertisement

“Haka kuma sojoji sojoji sun ƙwato bindigogi biyar samfurin maƙeran karkara, sai kuma wata babbar jaka da aka samu cike da wani garin da ake zargin tabar wiwi ce.

An ƙwato kwale-kwale mai ƙarfin dawakai 75.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending