Connect with us

News

Kotu Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yi Wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa Abdullahi Ganduje

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta jingine dakatarwar da aka yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a mazabarsa.

Mai Shari’a Abdullahi Liman ya umarci shugabannin Mazaɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, kada su yi aiki da umarnin babbar kotun jihar na dakatar da shugaban jam’iyyar.

Babu Ɓullar Sabuwar Cuta A Jihar Kano —Ma’aikatar Lafiya

Umarnin Babbar Kotun Tarayyar na zuwa ne awa 24 da babbar kotun jihar ta amince da bukatar shugabannin mazabar ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, saboda gwamnatin jihar mai ci na zarginsa da almundahana.

 

Advertisement

Alƙalin ya hana duk waɗanda umarnin kotun jihar ya shafa bin umarnin, har sai ya saurari ƙarar da Ganduje ya shigar gabansa ne neman adalci a saurari ɓangarensa.

 

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan nan na Afrilu domin sauraren buƙatar ta shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Kano.

 

Shugabannin APC na mazaɓar Ganduje da lauyan shugaban na APC, Jazuli Mustapha, ya shigar ƙara su ne Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da kuma Abubakar Daudu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending