Connect with us

News

Babu Ɓullar Sabuwar Cuta A Jihar Kano —Ma’aikatar Lafiya

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ja hankalin al’umma kan wani labari da wata jarida a arewacin Najeriya ta wallafa wanda ta ce wai an samu ɓullar sabuwar cuta a Kano da ta kashe mutane 45 a Gundutse da ke karamar hukumar Kura.

A martani na gaggawa game da tashin hankali da fargabar da lamarin ya jawo wa mutane, ma’aikatar, a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar Ibrahim Abdullahi ya tura wa da Jaridar Inda Ranka, ya ce ɗan jaridar ya karkatar da labarin ne domin cimma buri na ƙashin kai.

A rana irin ta yau ce  Manjo Gideon Gwaza Orkar ya ba da sanarwar ya kori jihohin Kano, Sakkwato, Katsina, Borno, Bauchi daga Nigeria

Sanarwar ta bayyana cewa, ɗan jaridan ya je ma’aikatar a ranar Talata 16/4/2024 domin daidaita labarin kuma an shaida masa cewa babu wata baƙuwar cuta a ko ina a jihar har, inda har jami’in da ke sa ido kan ɓarkewar cututtuka da sanar da su na jihar (SDSNO) aka buga waya domin bayyana hakiƙanin halin da ake ciki a yankin.

SDSNO, sanarwar ta ci gaba da cewa ya tabbatar da cewa cutar zazzabin cizon sauro da taifot ne ke ci gaba da wanzuwa a yankin, kuma za a bai wa ɗan jarida rahoton, amma abin takaici maimakon ya dakata kaɗan sai kawai ya ke ya buga labarin da ba gaskiya ba da ya sanya tsoro a cikin mutane.

 

Advertisement

Sanarwar ta bayyana cewa a cikin wani saƙon imel da Sashen Kula da Cututtuka na Ma’aikatar ya aika wa hukumomin da suka kamata da masu ruwa tsaki a ranar 8 ga Afrilu, 2024 mai taken Rahoto kan Halin Barazanar Rayuwa a Tsakanin Yara a Gainawa ‘A’, Gundutse, ya bayyana cewa biyo bayan rahotannin da ke aka samu na barazanar rayuwar yara a wannan gari, an samar da wata tawaga, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Lafiya a Matakin Farko (PHCC) ta ƙaramar hukumar Kura ta gudanar da cikakken binciken gaggawa domin kamo bakin zaren lamarin a kan lokaci.

 

Sashen ya ce binciken ya bayyana cewa ƙalubalen tsaftar muhalli da yankin ke fuskanta shi ke ƙara ta’azzara matsalolin kiwon lafiya da inda aka samu rahoton mutum goma sha uku sun kamu da kuma mutuwar mutane biyar, da abin ya fara tun daga watan Maris din 2024.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa jinkirin zuwa cibiyar lafiya da ke kusa daga al’ummar yankin ya ƙara dagula lamarin, ɗabi’ar da mafi yawan mutane ke da ita da ke haifar da cututtuka da mace-mace a cikin al’umomi da dama.

 

Advertisement

Rahoton ya ce, “Alamomin zazzaɓi mai tsanani da ciwon kai a tsakanin yara a yankin sun kasance suna faruwa a tsawon lokacin da aka bayyana. Binciken asibiti ya tabbatar da kamuwa da cutar zazzaɓin cizon sauro da taifot wanda ke nuna buƙatar gaggawa da ake da ita ta kai ɗauki don hana ci gaba da yaɗuwa da kuma asarar rayuka.

 

“Babbar cibiyar samar da ruwan sha ta yankin, wato rijiyar burtsatse, na cikin barazanar gurɓata ayyukan tsaftar muhalli da cunkoso sun zama wuraren ƙyanƙyasar sauro. Waɗannan abubuwan sun taimaka wajen yaɗuwar cututtukan da taɓarɓarewar lafiyar jama’a.

 

“Matakan da aka ɗauka a lokacin sun haɗa da kai ziyarar bayar da shawarwari, gudanar da cikakken bincike, ɗaukar samfurin jini don yin gwajin zazzabin cizon sauro da na Lassa (da sakamako ya nuna ba ko ɗaya), samar da magunguna da sauran kayayyaki kyauta don shawo kan cutar da fesa sinadarin kulorin a muhallin, komar da marasa lafiya babban asibiti, samar da isassun ma’aikata don gano cutar da wuri, haɓaka sanya ido da sadarwa a tsakanin al’ummar yankin da shigo da su ka’in da na’in.

 

Advertisement

“Muna ba da shawarar ɗaukar samfura da nazarin tushen samar da ruwan sha na yankin da fesa sinadarin kulorin cikin ta, tsabtace muhalli da ayyukan tsafta, sannan ana matuƙar buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da suka kamata don rage yaɗuwar cutar da.

 

“Bisa la’akari buƙatar gaggawa game da lamarin, mun buƙaci ma’aikatun muhalli da albarkatun ruwa da su hanzarta magance matsalolin lafiyar muhalli da aka bayyana a baya.

 

“Kai ɗauki a cikin gaggawa na da mahimmanci wajen kare lafiyar al’ummar yankin, musamman ma yara masu rauni waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa da cututtuka masu barazana ga rayuwa.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending