Connect with us

News

Masu garkuwa da mutane sun bindige Farfesan Jami’ar Babcock tare da yin garkuwa da wasu mutane biyu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe Farfesa Yinka Olomojobi, farfesa a fannin shari’a a jami’ar Babcock da ke Ilisha a jihar Ogun, tare da yin garkuwa da wasu mutane biyu.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da maharan suka mamaye yankin Iperu na jihar.

Harin Yan Bindiga Ya Sa Al’ummar Bini Gudun Hijira Zuwa Fadar Gwamnatin Jihar

Masu garkuwa da mutanen, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun yi niyyar sace Olomojobi, amma an harbe shi har lahira .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama mutum guda da hannu a lamarin.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending