News
Harin Yan Bindiga Ya Sa Al’ummar Bini Gudun Hijira Zuwa Fadar Gwamnatin Jihar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Daruruwan mutanen da suka tsere daga kauyen Bini da ke yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, sun taru a fadar gwamnatin jihar da ke garin Gusau don neman gwamnati ta samar musu da tsaro.
Radiyon Faransa ta ruwaito cewa a jiya Lahadi ne mutanen wadanda yawancinsu mata da kananan yara ne, suka dauki matakin hakan bayan janye sojoji da aka yi daga garin.
Daya daga cikin mazauna garin Malam Umar Salisu, ya ce a baya akwai sojoji a garin nasu, sai dai ‘yan bindiga sun kashe wasu daga cikinsu sannan a ranar Lahadi aka kwashe sauran da ke nan, don haka suka yanke shawarar kwasho dukkanin iyalansu zuwa fadar gwamnatin jihar don ta samar musu da tsaro.
A lokacin da kwamishinan kimiya da fasaha na jihar Alhaji Wadatau Madawaki ke wa mutanen bayani a madadin gwamnan jihar, ya ce ‘yan bindigar sun kara matsa kaimi wajen kai hare-hare ne saboda matakin gwamnatin jihar na kin yin sulhu da su.
Matawaki ya ce gwamnati ta tsara shirin yadda za a maida mutanen garinsu tare da rakiyar jami’an tsaro.
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a shiyar Arewa maso Yammacin Najeriya, inda hare-haren ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba wasu dabunnai da muhallansu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
