Connect with us

Uncategorized

Gidauniyar Lado Development Foundation Taba Sama Da Ɗalibai 200 Tallafin kuɗin Makaranta A Jami’ar Usman Ɗan Fodio Sokoto

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Sama Da Ɗalibai 200 Yan Jihar Kastina da suke Jami’ar Usman Ɗan Fodio Sokoto suka amfana da Tallafin kuɗin Makaranta Daga Gidauniyar Lado Development Foundation

Advertisement

Sama Da Ɗalibai 200 Yan Jihar Kastina da suke Jami’ar Usman Ɗan Fodio Sokoto suka amfana da Tallafin kuɗin Makaranta Daga Gidauniyar Lado Development Foundation

Lauyoyi A Kano Sun Shigar Da Kara Kan Kungiyar Lauyoyi Ta Kasa NBA

Dalibai ƴan asalin jihar Katsina masu karatu a jami’ar Ɗan fodiyo da ke birnin Sokoto sama da 200 sun amfana da tallafin kuɗin karatu a fannoni da dama na ilimi

Advertisement

Daliban dai sun samu wannan tallafi ne daga gagarumar Gidauniyar nan ta Lado Development Foundation saboda duba da matsin tattalin arziki da al’umma suke ciki yasa wannan Gidauniya ta duƙufa domin Ganin Dalibai yan Asalin Jihar Katsina sun cigaba da karatun su a ko’ina a faɗin Najeriya ba tare da fuskantar matsala ba

Bugu da ƙari wannan Gidauniya tayi kaurin suna wajen tallafawa Al’ummar jihar Katsina ta kowanne fannin cigaban rayuwar su, Wadda suka haɗa da fannin lafiya, ilimi, tallafin kuɗi hannu, da dai sauransu, sannan wannan gidauniya tana bawa Matasa, Mata, Tsofaffi da ƙananan yara muhimmanci sosai domin matsayin su a cikin al’umma, Ko a kwanakin baya Gidauniyar ta tallafawa dalibai masu dimbin yawa a jami’o’i da dama da suka haɗa da na cikin jihar da wajen ta.

Advertisement

Wannan ne ma ya sa kungiyar Ɗaliban jihar Katsina Reshen Jam’iar Ɗan fodiyo dake Sokoto suka karrama Gidauniyar da lambar Yabo na Musamman Saboda ƙoƙarin Gidauniyar a ɓangaren ilimi a jihar Katsina a lungu da saƙo

kuma duk wannan ayyukan suna daga cikin Burin Gidauniyar na ganin al’ummar jihar Katsina sun samu Cigaba ta fannoni da dama ta yadda jihar Katsina za ta zama abin kwatance a duk faɗin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending