Connect with us

News

Badakalar daukan aiki: Kotu ta daure Kwamandan Hukumar NSCDC na shekara biyar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wata kotu a jihar Katsina ta daure kwamandan hukumar tsaro ta ‘Civil Defense’ biyo bayan gurfanar da shi da hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa tayi.

Advertisement

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ICPC ta gurfanar da kwamandan mai suna Christopher Oluchukwu bisa tuhumarsa da hannu dumu-dumu a badakalar daukan aiki a hukumar NSCDC.

Hukumar EFCC:Ma’aikacin Kotu Ya Shiga Tasku Bayan Sama Da Faɗi Da Naira Miliyan 3.8

A karar da ICPC ta shigar, ta zargi Oluchukwu da karbar kudi N200,000, da N300,000 da N400,000 daga wurin wasu mutane uku da ‘ya’yansu ke neman aiki a hukumar NSCDC.

Advertisement

Iyayen masu neman aikin sun shigar da korafinsu a gaban hukumar ICPC bayan Oluchukwu ya gaza samarwa ‘ya’yansu aiki sannan kuma ya gaza dawo musu da kudinsu.

Lauyan hukumar ICPC, Ibrahim Garba, ya sanar da kotu cewa laifin da Oluchukwu ya sabawa sashe na 8, da na 10 da na 19 na kundin yaki da cin hanci da rashawa na shekarar 2000.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending