News
Shugabannin Kasashe Da Wasu Fitattun Mutane 26 Da Suka Mutu Sakamakon Hatsarin Jirgin Sama.
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Shugabannin Kasashe Da Wasu Fitattun Mutane 26 Da Suka Mutu Sakamakon Hatsarin Jirgin Sama.
1. Shugaba José Félix Estigarribia na kasar Paraguay ya mutu a hatsarin Jirgin sama a ranar 7 ga watan Satumba shekarar 1940.
2. Shugaba Ramon Magsaysay na kasar Philippines, ya rasa ransa a hatsarin Jirgin sama a ranar 17 ga watan Maris shekarar 1957.
3. Mista Nereu Ramos, shugaban kasar Brazil, ya mutu sanadiyar hadarin Jirgin sama a Ranar 16 ga watan Yuni shekarar 1958.
4. Shugaba Abdul Salam Arif na IRAQI ya rasu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 13 ga watan Afrilu shekarar 1966.
5. Shugaba Humberto de Alencar Castelo Branco na kasar Brazil shima ya mutu a ranar 18 ga watan Yuli shekarar 1967.
6. René Barrientos,/shugaban kasar Bolivia, ya rasa ransa a ranar 27 ga watan Afrilu shekarar 1969, a hatsarin Jirgin Shalkwafta
7. Ahmed Ould Bouceif, shugaban mulkin soji na kasar Mauritania, ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 27 ga watanJanairu shekarar 1979.
8. Shugaba Jaime Roldós Aguilera na kasar Ecuador ya mutu sanadiyar hatsarin Jirgin sama a ranar 24 ga watan Mayu shekarar 1981.
9. Janar Omar Torrijos, shugaban mulkin soji na kasar Panama ya mutu a ranar 31 ga watan Yuli shekarar 1981 sakamakon hatsarin Jirgin sama.
10. Shugaba Samora Machel na kasar Mozambique ya rasa ransa a ranar 19 ga watan Oktoba shekarar 1986 sakamakon hatsarin Jirgin sama, ko da ya ke akwai kokwanto kan hatsarin.
11. Shugaba Muhammad Zia-ul-Haq na kasar Pakistan ya mutu a ranar 17 ga watan Agusta shekarar 1988 sakamakon hatsarin Jirgin sama, ( sai dai akwai kokwanto akan wannan ).
12. Shugaba Juvénal Habyarimana na kasar Rwanda, ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 6 ga watan Afrilu shekarar 1994, bayan da aka harbo Jirgin da ya ke ciki da makami mai linzami.
13. Shugaba Cyprien Ntaryamira na Burundi, shima ya mutu a ranar 6 ga watan Afrilu shekarar 1994, bayan da aka harbo Jirgin da ya ke ciki da makami mai linzami.
14. Shugaba Boris Trajkovski na kasar Arewacin Macedonia, ya rasa ransa sanadiyar hatsarin Jirgin sama, a ranar 26 ga watan Fabrairu shekarar, sanadiyar hatsarin Jirgin sama.
15. Mai Alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Maccido Abubakar na III, ya rasu sakamakon hatsarin Jirgin sama a wani waje da ke kusa da birnin Tarayya Abuja, a ranar 29 ga watan Oktoba shekarar 2006.
16. Shugaban kasar Poland na karshe da ke gudun hijira a kasashen waje, Ryszard Kaczorowski, ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 10 ga watan Afrilu shekarar 2010.
17. Sebastián Piñera, tsohon shugaban kasar Chile, ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin shalkwafta, a ranar 6 ga watan Fabrairu, shekarar 2024.
18. Arvid Lindman, tsohon Firaministan kasar Sweden, ya rasu sakamakon hatsarin Jirgin sama, a ranar 9 ga watan Disamba, shekarar 1936.
19. Władysław Sikorski, firaministan kasar Poland da ke zaman gudun hijira a ketare, ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 4 ga watan Yuli shekarar 1943 – (Sai dai akwai kokwanto)
20. Barthélemy Boganda (Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ), ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 29 ga watan Maris, shekarar, 1959 – (Akwai kokwanto)
21. Joël Rakotomalala (Fira-Minista na kasar Madagascar) ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin Shalkwafta, a ranar 30 ga watan Yuli, shekarar 1976.
22. Džemal Bijedić, ( Fira-minista na tsohuwar kasar Yugoslavia) ya rasa ransa sanadiyar hatsarin Jirgin sama a ranar 18 ga watan Janairu shekarar 1977.
23. Francisco de Sá Carneiro ( Fira-Minista na kasar Portugal ), ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 4 ga watan Disamba, shekarar 1980. (Ana kokwanto)
24. Rashid Karami ( Fira-Minista na kasar Lebanon), ya mutu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 1 ga watan Yuni shekarar 1987, sakamakon harin bom da aka kai wa Jirgin da ya ke ciki.
25. Abdul Rahim Ghafoorzai (/Fira-Minista na kasar Afghanistan bangaren ‘yan tawayen Northern Alliance), ya rasu sakamakon hatsarin Jirgin sama a ranar 21 ga watan Agusta shekarar 1997.
26. Shugaba Ebrahim Raisi na kasar IRAN ya rasa ransa sakamakon hatsarin Jirgin Shalkwafta a ranar 19 ga watan Mayu shekarar 2024.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
