News
Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Hawan Babbar Sallah A Dukkanin Fadin Jihar Kano Baki Daya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN TUKUNTAWA
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar kano ta ce ta haramta hawan sallar yayin bukukuwan Babbar Sallah a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu.
Da Dumi Dumi : Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sauraren Shari’ar Masarautar Kano
Sanarwar ta ce rundunar ta dauki wannan matakin ne sakamakon barazanar tsaro da za a iya samu idan an gudanar da hawan sallar.
” Bayan ganawa da duk masu ruwa da tsaki a jihar kano, Rundunar yan sandan jihar kano ta hana yin duk wani hawa a yayin bikin sallah babbar dake tafe” a cewar Sanarwar.
Rundunar ta ce ta haramta hawan a dukkanin fadin jihar kano baki daya.
Rundunar ta bukaci al’ummar jihar da su gudanar da sallar idin su cikin kwanciyar hankali da lumana a inda suke, su kuma cigaba da baiwa rundunar hadin kai don cigaba da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
