News
Kano Civil Society Forum Ta Rantsar Da Sabbin Shuwagabannin Kungiyar Bayan Shekara 11
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gamaiyar Kungiyoyin farar hula ta Kano wato Kano Civil Society Forum (KCSF) ta rantsar da Sabbin shuwagabannin da za su gudanar da Kungiyar bayan shekara 11 a karkashin tsarin Shugabancin riko.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Taron rantsar war ya gudana ne a cibiyar ‘yan jarida ta NUJ da ke Kano a ranar Talata.
Zamanantar da Ayyukan Hukumar Kwastom Babban Cigaba ne A Najeriya
A jawabin Shugaban Kungiyar Muhammad Bello, wanda shine shugaban cibiyar binciken kirkire-kirkire da ci gaban Afirka wato African Center For Innovative Research and Development ya ce ya na mai gode wa kungiyar bisa wannan aiki da aka ba shi, kuma ya yi kira da a hada kai a tsakanin mambobin domin ciyar da manufofin kungiyar gaba.
Ya ce Kungiyar tuni ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki akan harkar Shugabanci wajen ganin an warware dukkan matsalolin da su ke addabar Kungiyar.
Haka zalika Fatima Musa, shugabar ayyuka ta Bridge Connect Africa Initiative, a matsayin mataimakiyar shugaba-1, yayin da Kabiru Ibrahim ya zama mataimakin shugaban kasa-2. Sai kuma Salisu Yusuf shugaban kungiyar kare al’umma ta Kano Social Protection Platform, sannan kuma da Aminu Sani Muhammad a matsayin mataimakin sakatare janar.
Sauran wadanda aka rantsar sun hada da Maryam Garba a matsayin Ma’aji da Umar Musa a matsayin mai ba da shawara kan harkokin shari’a.
