News
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero Ya Daga Tuta A Fadar Nassarawa
XAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya daga tutar mulki a karamar fadar da ke unguwar Nassarawa inda yake zaune.
A bisa al’ada, tutar na zama ne a matsayin alamar iko, kuma daga ta na alamta cewa sarki yana cikin fada.
Asusun Ba Da Lamunin Ilimi Na Najeriya NELFUND Ya Amince Da Bayar Da Lamunin Ɗalibai
Wannan kuwa na zuwa ne duk da umarnin gwamnatin Kano ga Sarki Aminu ya fice daga fadar a yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano.
Akan daga tutar ce da misalin karfe 6 na safe a kuma sauke ta 6 na yamma ko idan sarki ya yi bulaguron aiki.
Aminiya ta gano cewa ba a daga tutar ba a Fadar Nassarawa ba sai a safiyar Alhamis, duk da cewa an sanya karfenta a safiyar Laraba.
An yi ta ji-ta-ji-ta ranar Laraba cewa an sanya tutar, amma Aminiya ta gano cewa karfen kawai aka sa, Alhamis da safe kuma aka daga tutar.
Daga tutar a karamar Fadar Nassarawa na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da shari’ar da Gwamnatin Kano ke neman kotu ta hana Aminu Ado Bayero Aminu gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kano bayan ta maye gurbinsa sa Muhammadu Sanuni II, Sarkin Kano na 16.
Gwamnatin jihar ta je kotu ne tana neman a hana duk sarakuna biyar da ta rushe masarautunsu a jihar gabatar da kansu a matsayin sarakunan masarautun.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
