Connect with us

News

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa Da Dalibai Sun Bukaci Mambobi Su Kauracewa Shirin Gudanar Da Zanga-Zanga

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gamayyar Kungiyoyin Matasa da Dalibai na Arewa sun janye daga shirin gudanar da zanga-zangar adawa da tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da ita a Najeriya.

Advertisement

Gamayyar wacce ta dauki wannan mataki a taronta na kwanaki biyu a Kano, don haka ta umurci mambobinta da kada su shiga cikin ayyukan da aka shirya fara daga karshen watan nan.

Gobara Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Iyalan Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Na Kano

Da yake yi wa manema labarai a karshen taron a ranar Talata, Kodinetan kungiyar na kasa Jibril Sani Bello Gama ya bayyana cewa ba za su shiga zanga-zangar ba saboda  hakan zai cutar da dalibai sosai daga shiyyar Arewa Maso Gabas, wadanda suka sha fama da matsalolin ‘yan ta’adda na tsawon shekaru 13.

Advertisement

“Ya ku ‘yan uwa dalibai da matasa, ina kira gare ku da ku guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan. Ba a san wadanda suka shirya wannan zanga-zangar ba, kuma ba mu da tabbas ko manufarsu ta zaman lafiya ce ko ta tashin hankali.

“Wannan gwamnatin ta nuna kulawa ga dalibai ta hanyar samar da rancen ilimi ba tare da riba ba, tare da tabbatar da cewa zaku iya mayar da hankali kan karatun ku a yanzu kuma ku sami ayyukan yi a nan gaba don biyan wadannan lamunin.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa, wasu kungiyoyi  sun fitar da sanarwa ga ‘yan Najeriya inda suka bukaci da su shirya daukar matakin da ya dace a daukacin fadin kasar domin nuna rashin jin dadinsu da yadda gwamnati ke nuna halin ko-in-kula da al’umma ke ciki wajen magance matsalar rashin tsaro da fatara da yunwa da dai sauransu. al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending